(ABNA24.com) Mai magana da yawun ofishin wakilcin Iran a Majalisar Dinkin Duniya Ali Riza Miryousefi ne ya bayyana matakin na kin jinin Iran da cewa;kyakkyawan misali ne na siyasar rashin ‘yan adamtaka ta Amurka, wanda ya samo asali daga kiyayya da al’ummar Iran.
Miryousefi ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa; Kakaba sabbin takunkumai akan al’ummar Iran da ke fada da cutar Corona, kuma a lokacin da ake kara samun masu yin kira da a dage wa Iran din takunkumi a duniya, ba komai ba ne illa manuniya akan siyasar rashin ‘yan adamtaka ta Amurka,wacce ta samo tushe daga kiyayya ga Iran.
Amurka ta kakaba sabbin takunkumai 20 ga kamfanoni da jami’an Iran da Iraki, duk da cewa duniya tana yin matsin lamba ga Amurkan da ta dauke takunkumin da ta kakabawa kasar Iran wacce ta ke fada da cutar corona.
/129
30 Maris 2020 - 08:05
Lambar labari: 1021729
Mai magana da yawun ofishin wakilcin Iran a Majalisar Dinkin Duniya Ali Riza Miryousefi ne ya bayyana matakin na kin jinin Iran da cewa;kyakkyawan misali ne na siyasar rashin ‘yan adamtaka ta Amurka, wanda ya samo asali daga kiyayya da al’ummar Iran.